Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwanaki 10 Na Karshen Watan Ramadan Na Dauke Da Falala Mai Yawa


Malan Mukhtar Sharada
Malan Mukhtar Sharada

Malan Muktar Umar Shara, Limamin masallacin Juma’a na Rijiyar Zaki – ya ce manzo Allah SAW ya ce watan ramadana, na dauke da daren lailatul kadar, dare da yayi daidai da dare dubu a cikin shekara, a inda manzon rahama yake bukatar al’ummarsa da su jajirce wajen raya watan na ramadana.

Ya ce an baiwa al’ummar manzon Allah, wannan dare mai albarka domin samun falala, sannan an ware wannan daren ne a mara, inda mafi yawan al'umma ke shagala da sakankacewa har sai goman karshe a wasu daidaikun ranaku

Mal Muktar, ya ce an so al'umma su raya dukkanin watan gaba daya, maimakon zaben wasu lokuta da ake sa ran za’a riski wannan daren, sabanin damar raya wasu ranaku a goman karshe.

Akwai butara jama'a su tashi tsaye wajen raya kwanakin karshen wannan watan do neman dacewar da rahamar Allah. Ku biyu mu domin jin cikakkiyar hirar mu da Malan Muktar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG