Biyo bayan karatun tanatsu da suka yi ya sa sun tattara kawunansu wuri guda domin su tabbatar sun zabi shugabanni nagari a zabuka dake zuwa a shekarar 2015 idan Allah ya kaimu. Suka ce idan aka cire masu masaukinsu to babu wata al'umma da ta kai yawansu. Amma a kowane zabe sai a yi yaki a barsu da kuturun bawa. Suka ce wannan ya sa suka hada kai suka kafa kungiyar su tabbatar cewa koina suke sun zabi shugaba nagari wanda ba zai yi jifan mataccen mage da su ba bayan zabe.
Shugaban kungiyar Alhaji Zubairu Mohammed Haruna ya yi karin bayani. Ya ce suna da abubuwa a gabansu da suka shafi kasuwanni da siyasa da zamantakewar jama'a. Don haka suka hada kansu su zabi shugaba nagari wanda zasu sameshi ya yi alkawarin abun da zai yi masu su ma su yi masa. Amma ba zasu yadda a yi anfani da jama'arsu ba bayan zabe idan sun je neman abu a hanasu.
Rashin hadin kan 'yan arewa sabili da rububin neman sarauta ya sa kowa wainarsa yake toyawa. Sakataren kungiyar Malam Abdulkarim Murtala Zaria ya ce sun gane yanzu cewa basu da shugabannin da zasu kwato masu 'yancinsu. A kan banbancin addini da kabilanci dake tsakanin 'yan arewa ya ce sun kafa kwamitoci. Kwamiti daya zai taimaki kungiyar lalubo yadda harkar addini ko kabilanci bai taso ba. Malam Umar Mohammed Azinge da ya wakilci mutanen Ibadan ya ce sun dade suna tafiya a makance musamman idan lokacin zabe ya zo inda shugabannin kadai ke anfana. Lokaci ya yi yanzu da zasu gyara alamura. Ya ce zasu bi duk 'yanuwansu dake jihohi shida na yammacin kasar kada su yadda a yi masu dodorido domin su canza alkibla.
Ga karin bayani.