Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Kira Ga Sudan Ta Bayar Da Yanci Ga Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Dafur


Shugaban yan tawayen Sudan Ta Kudu Riek Machar
Shugaban yan tawayen Sudan Ta Kudu Riek Machar

Shugabannin Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Afirka sun yi kira da babbar murya ga kasashen, sun yi kira ga kasar Sudan da su bada damar ‘yanci da walwalar rundunar kiyaye zaman lafiya da kuma jami’an agaji a Darfur, garin da dubban jama’a suka rasa muhallansu a sakamakon yaki.

Wata sanarwar hadin gwiwa daga Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugabar Kungiyar Kasashen Afirka Nkosazana Dlamini tace, “Ba wani matakin soja na warware rikicin Dafur har yanzu, sannan muna kira ga dukkan bangarorin kasar da su dukufa don tattaunawar da zata kawo zaman lafiya a kasar”.

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane fararen hula guda 90,000 ne yakin na tsakanin sojojin gwamnati da ‘yan tawaye yaraba da gidajensu a Arewacin Darfur a cikin makonni 6 na rikicin.

Sai dai Majalisar ta Dinkin Duniya bata tabbatar da maganar ‘yan gudun hijira guda 50,000 da aka ce ba, sakamakon an hana ma’aikatan agaji kutsawa yankin.

Amma duk da haka yakin na yankin Darfur da aka fi shekaru 10 ana yinsa karkashin jagorancin larabawan kasar ‘yan yakin sa kai, ya haifar da mutuwar mutane akalla guda 300,000 da kuma samar da ‘yan gudun hijira sama da Miliyan 2 da Dubu 600.

XS
SM
MD
LG