Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara zuwa kasar Kamaru, a yau talata don tattaunawa da takwararsa na kamaru Mr Paul Biya a wani yunkuri na hadin gwiwa don yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram, dake addabar kasashen.
Gwamnonin jihohin Adamawa da Borno, zassu kasance cikin tawagar Shugaba Buhari, a wannan ziyarar aikin da zai kai akan matsalar Boko Haram, ganin cewa wadannan jihohi na makwabtaka da kasar Kamarun.
Kafin wannan ziyarar ta kasar Kamaru, saida shugaba Buhari ya kai makamashi wannan ziyarar zuwa kasashen jamhuriyar Niger da Chadi, a makon san a farko da fara aiki a matsayin shugaban Najeriya.
Gwamnan jihar Adamawa wanda ya tabbatar da wannan ziyarar da zasu kai ya bayyana wa wakilin muryar Amurka, Ibrahim Abdulaziz cewa jihar Adamawa da kasar Kamaru ana cudanya da juna da kasuwanci batare da wani tsagwama ba.
Wannan na zuwane a daidai lokacin da jama’ar, jihar Adamawa, ke yabawa Bankin duniya da kuma kasar Amurka, bisa alkawarin tallafi dan tada komadar tattalin arzikin al’umomin yankin da fitinar ‘yan Boko Haram ya addaba.