Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Kan Shugabanci Matasan Najeriya Tsakanin Kudu da Arewa


Matasa
Matasa

An kaure da hayani a wurin taron matasa na kasa da ake gudanarwa a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, tsakanin matasa daga arewacin da kudancin Najeriya.

Hayaniyar dai ta samo asalin ne dagane da shugabanci kungiyar ta matasan Abdullahi Aliyu Katsina, wakili daga arewacin Najeriya, a hirar su da wakilin muryar Amurka, Hassan Maina Kain, yace “ Abunda ya faru shine maganar shugabanci wanda kusan kowane lokaci shike da tasiri a abunda za’a yi wanda zai kawo sakamako ingantatce, a hakikanin gaskiya mun kasance mu muka fi kwararrun mutane a cikin wannan taro amma saboda wasu dalilai an yi kokari ayi satar shugabanci ta bayan fagge, mu kuma munga cewa ba daidai bane.”

Ya kara da cewa a matsayi mu na ‘yan arewa bamu yada muka juyawa wannan alamari baya ba sai wannan lokaci dalili kuma shine muna ganin cewa ayi tayi kura kurai amma a yanzu bai kamata abamu shugaban da bai dace ba.

Barrister Aremu Oladotun Hassan, shugaban matasan Yarbawan Najeriya, kuma wakili a wannan taron daga kudancin kasar yace irin wannan taro na matasa kowa na kare muradun sa ne.

Yana mai cewa amma duk da haka zamuyi kokarin ganin an shawo kan wannan fitinar.

Sai kuma tababar shekarun wakilin jihar Yobe a zauren taron Dauda Muhammad Gombe, da waasu wakilai daga kudancin kasar suka yi inda shugaban taron ya nemi shi wakilin matasan jihar Yoben da yazo yak are kansa.

Yace an haifeshi a shekarar 1987, a Damaturu, kuma dukkanin takardun shedata suna tabbatar da hakan.

XS
SM
MD
LG