Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ansu Fati Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakaru Ta El Clasico


Ansu Fati, jogador do Barcelona FC.
Ansu Fati, jogador do Barcelona FC.

Dan wasan Barcelona Ansu Fati ya kafafa damarsa a tarihin wasan jikakkiyar hamayya ta El-Clasico.

Fafatawar ta shekaran jiya Asabar ta yi kyau matuka, inda Federico Valverde ya fara zurawa Madrid kwallon farko, ya yin da Karim Benzema ya jefa masa kwallo shima ya cika aiki a dai-dai minti biyar da fara wasa.

Nan ne matashin na Barcelona Fati da ya shiga wasan minti uku kacal da ya maye gurbin Camp Nou, ya ware Jordi Alba ya tura masa kwallo, shi kuwa ya sakata a raga aka yi kunnen doki.

Wannan rawar gani da matashin ya taka ta bashi damar ci gaba da samun gurbi a fafatawar Clasico a matsayinsa na dan yaro da ya kafa tarihi a wannan karnin cikin wasan La Liga.

Ansu Fati
Ansu Fati

Kokarin da Fati ya yi shine na biyu wurin sake kafa wannan tarihi a cikin wannan shekarar, inda Vinicius Jr ya kafa wannan tarihin a cikin watan Maris yana mai shekaru 19 da kwanaki 233 a duniya.

APTOPIX Spain Soccer Champions League
APTOPIX Spain Soccer Champions League

A baya kuwa shahararren gwarzon kwallon kafa na Barcelona Lionel Messi, ne ya kafa wannan tarihin, a wasansa na farko tsakanin manyan kungiyoyin Barca da Madrid ,da suka raba rana da ci 3-3 amma shi sabon dan wasan ne ya zurawa Barca kwallaye ukun duka.

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG