Yara ‘yan kasa da shekara biyar da haihuwa sama da dubu takwas ke fama cutar tamowa a jihar Adamawa.
Bayanin na kunshe a alkaluman da asusun kula da lafiyar yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF tare da hadin gwuiwar cibiyar kula da lafiya ta matakin farko ta bayar, bayan taron karawa juna ilimi na yini biyu a Yola fadar jiha kan sabbin dabarun aikewa da bayanai kan cutar tamowa ta wayar selula.
Shugabar sashin samarwa yara da mata masu shayarwa abincin mai gina jiki Malama Hauwa Zoka ta shaidawa sashin Hausa cewa ko da yake cutar wadda ta fi yin tsanani lokacin damina, bana an sami karuwar yara masu fama da cutar sakamakon rikicin Boko Haram da ya raba mutane da muhallansu da kuma gonakinsu na lokaci mai tsawo.
Ta ce taron zai baiwa jami’an kiwon lafiya mataki na farko damar aika bayanai wa hukumomin da zai taimaka wajen daukar matakan gaggawa na hana cutar yaduwa.
Benjamin Martins da Ayina Elson wasu mahalarta bitar sun danganta cutar da rashin sanin yadda zasu sarrafa abincin yara a yankuna da suke da wadatar abinci da kuma al’adun gargajiya.
Wakilinmu ya zaga wata cibiya ta kula da yara da ke fama da tamowa na Jambutu a karamar hukumar Yola ta arewa inda ya iske iyaye dake karba jinya wa ‘ya’yansu da suka shaida ana kula da su daidai gwargwado.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.