Taron da ya wakana sanadiyar yunkurin babban sifeto janar na yan sandan Najeriya Ibrahim Idris na shawo kan matsalolin tsaro da kasar ke fama dashi, musamman a jihohin arewa maso gabashi.
Yankin yana fuskantar barazanar ayukan ta'addanci daga kungiyar Boko Haram kungiyar da ta kara kaimi wajen kai hare-hare a jihar.
Muryar Amurka tayi fira da wasu cikin mahalarta taron kuma ta fara taunawa da
shugaban 'yan banga na jihar Adamawa Dr, Murtala Aliyu wanda ya ba da
shawarwari ta yadda wannan sabon shirin zai dore ya kuma inganta tsaro a yankin arewa maso gabas musamman jihar Adamawa.
Shi kuwa Alhaji Sabo Magaji gani yake akwai bukatar
a kyautata aikin kananan 'yansanda masu hulda da jama'a yau da kullum ta hanyar da zasu himmatu su kuma dauki ayyukansu da mahimmanci ta kiyaye
tsaron lafiya da dukiyoyin jama'a.
Da yake mayarda martani wamishinan yan sanda na
jihar Adamawa yace hukumomi na daukan matakan da suka wajaba da zummar kawar da duk wani aika-aika.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.