Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Fiye Da 100 Sun Mutu A Fashewar Tanka A Najeriya


Wata tankar jigilar iskar gas ta girki ta haddasa mummunar gobara a wata tashar rarraba gas jiya a Najeriya, ta kashe mutane fiye da 100 da suka yi layi su na jiran cika bututun gas dinsu.

Wannan hatsarin ya faru a garin Nnewi dake kudancin Najeriya. Ya zuwa lokacin da 'yan kwana-kwana suka kashe wutar da ta tashi, wani wakilin kamfanin dillancin labarai na Associated Press yace ya kirga gawarwakin mutane fiye da 100 a wurin.

Wani shaida mai suna Emeka Peters, ya fadawa kamfanin dillancin labaran na AP cewa wutar ta tashi da misalin karfe 11 na rana a lokacin da wata tankar da ta sauke gas a tashar Chikason Group Gas, ta kama hanyar fita ba tare da ta tsaya ta yi sanyi kamar yadda ake yi ba.

Peters ya ce, "wutar ta tashi kamar wani bam. Duk tashar ta kama da wuta, yayin da bututun gas suka rika fashewa suna bindiga, hayaki baki kirin yana tashi sama. Mutane da yawa sun mutu, kuma akasarinsu wadanda suka yini suna yin layi ne domin sayen gas na girki."

Yace an dauki gawarwakin wadanda suka mutu da kuma wasu mutanen kalilan da suka ji rauni zuwa asibitin koyarwa na Jami'ar Nnamdi Azikiwe dake Nnewi.

XS
SM
MD
LG