Dandalinvoa ya sami zantawa da wata ‘yar gwargwarmaya mai aiki da kungiyoyi masu zaman kansu ne wajen fafatukar kare muhalli da wata kungiya mai rajin kare ma’adanai da ke karkashin kasa tare da tabbatar da gwamnati ta bi ka’idojin kare al’ummar da ke yankin da ke fama da matsalolin da suka danganci kasa inji Fatima Muhammad Umar.
Har illa yau tana aiki da kungiyar da take kula da harkokin matasa da harkokin mata duk da zummar kare hakkin mata da matasa, kasancewarta mace ta ce rayuwa sai da gwagwarma domin ganin ba’a tauye hakkin mata ko matasa ba.
Ta ce kasancewar tana cikin wadannan kungiyoyi, tana fuskantar matsaloli da dama a cewar malama Fatima Umar, musamman ganin yadda samun aikin gwamnati a Najeriya said an wane da wane, dan haka dan haka zata ci gaba da gwagwarmaya.
Ta kara da cewa kasancewar samun ilimi da wayewa na zamani, a yanzu ko da ta fuskanci kalubale ba ta bari ya tauye ta ko ya hana ta aiki.
Facebook Forum