Wani babban alkali ya gurfanar da Mark Adams Prieto mai shekaru 58 a ranar Talata bisa zarginsa da laifin safarar bindigogi domin amfani da su wajen aikata laifin nuna kyama da kuma mallakar bindiga mara rajista.
An tsayar da Prieto ne a ranar 14 ga Mayu yayin da ya ke tuki kan babbar hanyar New Mexico inda aka kama shi da bindigogi bakwai a cikin motarsa, a cewar ofishin da ke wakiltar gwamnatin Amurka na gundumar Arizona.
Tun da farko dai ya shaidawa wani jami’in hukumar FBI da ya fake a matsayin mai son nuna wariyar launin fata cewa ya shirya ya tuka mota zuwa birnin Atlanta na jihar Georgia domin leken asirin wuraren da za a iya kai wa hari, da nufin aiwatar da harin gabanin zaben shugaban Amurka a watan Nuwamba, a cewar tuhumar da ake masa.
Tsakanin watan Janairu da Mayu, Prieto ya gana akai-akai tare da wani jami'in sirri na FBI da wata majiya mai taimakawa FBI a asirce don nunin bindigogi daban-daban a kusa da Arizona.
Kafin watan Janairu, ya yi magana da jami’in FBI din da ke fake game da "kai harin kan Bakar fata, da Musulmai, da Yahudawa" a cewar karar.
Prieto ya shirya halarta wani bikin kide-kide a birnin Atlanta inda dimbim Amurkawa bakar fata za su halarta domin gudanar da harin.
Sai dai makonni kadan bayan haka, a wani wasan nuna bindiga a Phoenix, Prieto ya shaidawa jami'in FBI din cewa yana tunanin canza wurin harin zuwa masallaci, in ji karar.
Yanzu haka yana fuskantar hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari idan aka same shi da laifi..
Ba a samun jin ta bakinsa ba, yayin da lauyan da ke wakiltarsa bai amsa tambayoyin nan da nan ba.
Dandalin Mu Tattauna