Wata kara da aka shigar a jiya Lahadi na tuhumar mawaki kuma mai shirya fina-finai Jay-Z da yiwa matashiya ‘yar shekaru 13 fyade tare da tauraron wakokin gambara na hip-hop Sean Combs a shekarar 2000, kamar yadda bayanan kotu suka bayyana, zargin da Jay-Z ya musanta aikatawa.
Tuhumar da aka sabunta a kan Combs na zargin Jay-Z, wanda sunansa na gaskiya Shawn Carter da Combs sun aikata fyaden ne a shekarar 2000.
“Wani fitaccen mutum na tsaye yana kallo sa’ilin da Combs da Carter ke karba-karba wajen cin zarafin matashiyar. Akwai mutane da dama bayan kammala wata liyafa, amma babu wanda ya dauki mataki wajen dakatar da cin zarafin,” a cewar korafin da ake shigar.
Jay-Z ya maida martani ga lauyan daya shigar da karar, inda yake zargisa da zama mutumin banza.
Dandalin Mu Tattauna