Majalisar Wakilan Amurka mai rinjayen ‘yan jam’iyyar Demokrat ta shirya maida shugaban kasar dan jam’iyyar Refublikan, ya kasance shugaban Amurka na uku da za’a tsige a tarihin shekaru 243 na kasar, duk da yake har yanzu ana tababar yiwuwar tabbatar da tsige shi din a majalisar wakilai.
“Mun kammala aikin mu a majalisa,” dan majalisar wakilan Jerrold Nadler ya shaidawa shirin “This Week” na gidan talabijin din ABC News, kwanaki biyu bayan da kwamitin shari’a na majalisar da yake shugabanta, ya amince da daftari 2 na tsige shugaba Trump.
Kwamitin da ‘yan Demokrat suke da rinjayi, akan ‘yan Refublikan da suka hada kansu suke goyon bayan shugaba Trump, sun zargi shugaban da yin amfani da mukaminsa ba bisa ka’ida ba, ta hanyar neman Ukraine ta binciki daya daga cikin manyan abokan karawarsa na jam’iyyar Demokrat, tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, da kuma yin katsalandan ga zaman majalisar na binciken abin da ya aikata, ta hanyar kin bayar da kundin bayanai mai dubban shafuka ga masu bincike, da kuma hana manyan jami’an sa ba da shaida.
Trump ya kara kushe yunkurin na tsige shi a jiya Lahadi, inda ya bayyana bukatar sa ga shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy na gudanar da bincike da cewa kiran wayar tarho ne da ya dace da doka.
Facebook Forum