Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ta Gudanar Da Zanga-Zanga a Switzerland Kan Zuwan Donald Trump


Masu zanga-zangar kin jinin Trump a Switzerland
Masu zanga-zangar kin jinin Trump a Switzerland

Masu zanga-zanga na ta kwararowa kan tituna a wasu biranen kasar Switzerland, domin nuna adawarsu ga halartar da shugaban Amurka Donald Trump zai yi taron kolin tattalin arziki na kasashen duniya a Davos cikin wannan makon.

A yau Alhamis ne ake sa ran Trump zai isa kasar Switzerland, inda zai gabatar da sakon Amurka ta farko a jawabin zai yi gobe Juma’a gaban manyan ‘yan kasuwa na duniya da shugabannin siyasa.

A jiya Laraba ne, tawagar masu taimakawa Trump a fannin tattalin arziki su ka sake nazarin dabarun kara himmar Amurka a fagen gasar duniya.

A cewar mujallar Bloomberg mai tantance darajar dalar Amurka da sauran kudaden duniya, Sakataren baitulmalin Amurka, Steve Mnuchin, ‘daya daga cikin ministoci goma da suke halartar taron, ya amince da rage karfin dala.

Da yake magana da manema labarai a Davos, Mnuchin ya ce “rage karfin dala yana da alfanu garemu, idan aka kwatanta da cinikayya da kuma damar da zamu samu.”

Mnuchin ya ce “Wannan duk akan ajandar baiwa Amurka fifiko kafin wata kasa, amma Amurka baiwa Amurka fifiko na nufin aiki tare da sauran duniya, akan batun cinikayya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG