Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da NATO Sun yi Tir da Amfani da Makamai Masu Guba a Syria


Rex Tillerson-Sakataren Harkoki Wajen Amurka
Rex Tillerson-Sakataren Harkoki Wajen Amurka

Amurka ta karu da kawayenta na NATO a jiya Talata suka yi tir da amfani da makamai masu guba a kasar Syria, yayin da suka dora laifi a kan kasar Rasha mai bada kariya ga gwamnatin shugaban Syria Bashar al-Assad

Hari na baya bayan nan a kan Gabashin Ghouta ta tada hankali cewar gwamnatin Bashar al-Assad tana ci gaba da yin amfani da makami masu guba a kan a’ummarta, inji sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson yake fada a birnin Paris.


Tillerson yace akalla mutane 20 aka kashe a ranar Litinin a cikin wannan hari da aka kai da iska mai tsananin guba a yankin Gabashin Ghouta kusa da Damascus dake hannun yan tawaye.


Sai dai ya dora laifi a kan Rasha da kuma taimako da take yiwa gwamnatin Assad.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG