Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Tsauni Ya Barke da Wuta A Tsakiyar Kasar Japan


 Tsaunin Kusatsu-Shirane da ya barke da wuta yau Talata a tsakiyar kasar Japan
Tsaunin Kusatsu-Shirane da ya barke da wuta yau Talata a tsakiyar kasar Japan

Tsaunin da ake tseren dusar kankara a tsakiyar Japan ya barke da wuta yau Talata ya kuma yi sanadiyar raunata mutane da dama tare da bacewar alkalla mutum daya

Akalla mutum guda ya bata, sannan wasu da dama sun ji raunuka, bayan wani bala’in aman wuta da ya auku a yau Talata a wani tsauni da ake tseren dusar kankara a tsakiyar Japan, lamarin da ya haifar da zaftarewar tare da kwararowar dusar kankarar.

Bala’in wanda ya auku a da tsakiyar ranar yay Talata a tsaunin da ake kira Kusata-Shirane, ya sa duwatsu sun yi ta fadowa a yankin wanda ake shakatawa.

Da yawa daga cikin wadanda suka jikkata, suna zaune ne a yanki mai gangara a lokacin da hadarin aman wutar ya auku.

Akalla mutane hudu ne suka ji rauni sanadiyar duwatsun da suyka rika fadowa bayan da suka farfasa gilashin abin hawan da suke ciki.

Rundunar sojin kasar ta Japan sun ce akwai dakarunsu shida a cikin wadanda wannan bala’i ya rutsa da su, wadanda duk aka ceto su daga baya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG