Gwamnatin Najeriya na shirin linka kudaden harajin da ake kira VAT a turance, wato haraji akan duk wadanda suka yi sayayya da kuma tsaurara matakan canjin kudade.
Malam Kassim kurfi mai sana’ar hada-hadar hannun jari, ya fada ma muryar Amurka cewa tsaurara Matakan kasuwancin kudaden zai yi tasiri amma ba sosai ba. Ya kara da cewa an sami raguwar dala da kusan kashi arba’in cikin dari a Najeriya. Ya kuma ce, abinda ya kamata gwamnati tayi shine ta daga farashen dala yadda zai iya hana wadanda ke kasashen ketere fidda kudadensu daga Najeriya, kuma hakan zai sa wadanda ke waje su shigo da kudadensu abinda zai sa a sami raguwar farashen kayayyaki..
“A kasashen da suka cigaba, ana karbar kashi 10 zuwa 15 na harajin. Amma a kasa kamar Najeriya da ake so a yi karin kashi 10, aiwatar da wannan Matakin shine babbar matsala, saboda harajin bai zuwa inda ya kamata kuma gwamnati bata da Matakan da zata tabbatar da duk wani saye da sayarwar da ake yi” Inji Malam Kassim.
Bayan haka Malam Kassim yace a yanzu da ake shirin zabe, abubuwa irin wadannan na iya kawo bakin jini ga gwamnatin kasar.
kamar yadda za kuji a nan, ga hirar da Ladan Ibrahim Ayawa yayi da Malam Kassim Kurfi.