Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DAPCHI: Ba Za a Yi Watsi da Leah Sharibu Ba -Inji Buhari


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Yayin da ake cigaba da murnar sakin akasarin 'yan matan Dapchi da kuma juyayin rasuwar biyar daga cikinsu, Shugaba Buhari ya sha alwashin ceto yarinya guda da ta rage a hannun 'yan Boko Haram.

Yayin da iyaye da ‘yan’uwa da sauran masu ruwa da tsaki ke nuna damuwa saboda kin sakin daya daga cikin ‘yan matan Dapchi da ‘yan Boko Haram su ka kama, Fadar Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ta ce Shugaba Buhari ya himmantu ga kubutar da yarinya daya tilo din, kamar yadda ya dukufa ga kwato ‘yan matan, lokacin da dukkanninsu 110 ke hannun ‘yan Boko haram.

“Gwamnatin Buhari ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kubutar da Leah Sharibu da kuma maido da ita gida lami lafiya wurin iyayenta kamar sauran ‘yan matan bayan da ‘yan ta’addan su ka cigaba da rike ta saboda shawarar da ta yanke, kamar yadda rahotanni ke nunawa, na kin barin addininta na Kirista ta zama Musulma.”

Takardar bayanin ta jaddada cewa Shugaba Buhari ya na da cikakkiyar masaniya game da nauyin da ya rataya a wuyansa na kare kowani dan Najeriya ko da wani addini ya ke yi; ko da dan wani kabila ne kuma ko da daga wani sashin Najeriya ya fito; kuma Shugaba Buhari sam ba zai yi jinkiri kan wannan ba.

Sanarwar ta kara da cewa, “Haka zalika, Shugaba Buhari na mai la’akari da cewa Musulmi na zahiri a duk fadin duniya na biyayya da umurnin Musulunci mai cewa babu tilastawa a addini. Saboda haka bai kamata wasu su tilasta ma wasu bin addininsu ba.”

Sanarwar ta cigaba da cewa Shugaba Buhari na mai matukar tausaya wa iyayenta ganin cewa sun a ganin wasu iyayen na murna a yayin da su kuma Boko Haram ke cigaba da rike ma su diya. Shugaba Buhari ya kara jaddada ma iyayen yarinyar cewa zai cigaba da yin duk abin da ya ke iyawa wajen ganin ita ma Leah ta samu kubuta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG