Kawo yanzu akwai 'yan Najeriya dari hudu da 'yan kai a gabashin Kamaru inda babu mai kula da su. Neman tsira da rai ya kaisu kasar. Kamar yadda wasu daga cikin 'yan gudun hijiran suka bayyana akwai 'yan Najeriya fiye da dari hudu a garin Kinzuwa cikin karamar hukumar Bature a lardin Dituwa a gabashin kasar Kamaru. Domin basa samun kula suna rokon gwamnatin Najeriya ta kaimasu doki. 'Yan gudun hijiran sun koka da karancin abinci da magunguna da wuraren kwanciya. Wasu da yawa sun rasu wasu kuma suna cikin rashin lafiya.
Wani da aka zanta dashi mai suna Mustapha yace suna kan iyakar Kamaru ne da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kasar da suka guje ma domin a cewarsa ana kashe Musulmai. Yace da kyar suka samu suka ketara cikin kasar Kamaru. Masu gudun hijiran sun kai wajen dubu goma amma 'yan Najeriya cikinsu dari hudu ne da 'yan kai. Kawo yanzu babu wani jami'in diflomasiya na Najeriya dake kasar Kamaru da ya je ya gansu. Su kuma sun ce basu da takardun izinin tafiya da zasu je Yaounde babban birnin Kamaru inda Najeriya ke da ofishin jakadanci da jakada.
A wata sanarwa da hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya tace akwai kimanin 'yan gudun hijira dubu dari tara a Kinzuwa. Hukumar agaji ta Najeriya tace zata kai doki ga 'yan Najeriya dake Kinzuwa. Amma jami'in hukumar agajin mai kula da shiyar arewa maso gabas Alhaji Muhammed Kanar yace akwai matakan diflomasiya da dole sai an dauka. Yace wadanda suke kasar ta Afirka ta Tsakiya an daukosu kai tsaye amma wadanda suka sulale suka shiga wata kasa sai an bi hanyar diflomasiya gwamnatin kasar ta yadda da hanyoyin da aka tsara na zuwa daukosu. Akwai shugabannin kasa da kwamitin dake aikin kuma suna nan suna yi. Yace ba abu ne wanda mutum zai kama mota ya hau kamar yadda mu keyi cikin kasarmu. Dole sai kasashen sun ba Najeriya dama kana a je a daukosu.