Sambo Dasuki mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya bude taron. Taron zai duba yadda kasashen dake makwaftaka da Najeriya zasu tallafa mata wurin yaki da kungiyar Boko Haram, kungiyar da ta sha yin gumurzu da dakarun Najeriya a arewa maso gabashin kasar.
Shugaban hukuman kwastan na Najeriya Alhaji Abdullahi Dikko Inde wanda shi ne mai masaukin baki yayi karin bayani kan mahimmancin taron. Yace kowa ya san yadda kasar take yanzu. Mutumin jamhuriyar Niger ba zaka banbantashi ba da mutumin Katsina. Haka ma da wuya a banbanta mutumin Lagos da na kasar Benin ko Togo. Haka ma mutumin Calabar da Kamaru tamkar daya suke. Idan an juya arewa maso gabas babu banbanci tsakanin mutumin Maiduguri da Chadi.
Alhaji Inde yace a tashi hikimar ya ga ya kamata ya gayyato shugabannin kwastan na kasashen domin kowa ya san halin da Najeriya ta samu kanta. Yace da Najeriya da su kasashen babu mai kwamciyar hankali. Haka lamarin yake tsakanin mai shi da mara shi a kasar Najeriya yau, musamman a arewa maso gabas. Yace kodayake hankali ya koma ga Allah amma yakamata a gayyato hukumomin kwastan na kasashen yammacin Afirka su yi muhawara kan abubuwan da zasu iya yi domin shawo kan ta'adanci a kasar. Taro ne inda zasu bada gudunmawarsu kan yadda za'a samu masalaha.
Makasudin taron dai domin a samu hadin kai tsakanin mutanen hukumomin kwastan na Najeriya da Benin da Chadi da Kamaru da sauran kasashen da kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro domin a kawar da ta'adanci da sarafa miyagun kwayoyi da miyagun makamai da fataucin mutane da hana sumoga.
Akwai fargaban cewa wasu kasashe dake makwaftaka da Najeriya ka iya samun nasu kungiyar Boko Haram idan basu hada hannu da kasar ba domin kawar da kungiyar yanzu. Alhaji Inde yace sun fada masu kuma su ma suna sane da hakan. Idan suka bar Najeriya ta gyara nata matsalar abun na iya komawa kansu.
Shi ma shugaban kwastan na Jamhuriyar Niger Malam Muhammed Maji Maiyaki yace tabbas taron zai yi tasiri da kuma anfani wurin hada karfi da karfe a yaki ta'adanci da miyagun makamai da miyagun kwayoyi.
Ga cikakken rahoto.