Wakilin Muryar Amurka a Maiduguri, Haruna Dauda, yace yau litinin da rana ne labari ya bazu a cikin Maiduguri cewa an sako Dr. Monguno, kuma ya komo gida. Hukumomi sun ce an sako shi a yankin Marte, ya kuma komo gida tare da direbansa,
Wakilin namu ya ce ya ga Dr. Monguno cikin koshin lafiya, sai dai alamar gajiya da ya gani a jikinsa kawai. Dr. Monguno bai yi magana ba, amma iyalinsa sun nuna farin ciki tare da godiyar sako shin da aka yi.
Mataimakin gwamnan Jihar Borno, Alhaji Zanna Umar Mustapha, ya bayyana cewa ba a biya ko sisin kwabo domin sako dattijon ba. yace wadanda suka sace shi, su ne suka sako shi domin radin kansu, musamman a bayan rokon da jama'a suka yi.
Ga rahoton na Haruna Dauda daga Maiduguri: