Al’ummar Nigeria, musamman na jihar Borno da birnin Maiduguri, na ci gaba da bayyana jin takaici da awon gaba da aka yi da dattijo Dr. Shettima Ali Munguno bayan gama sallar jumu’a.
WASHINGTON, DC —
Al’ummar Nigeria, musamman na jihar Borno da birnin Maiduguri, na ci gaba da bayyana jin takaici da awon gaba da aka yi da dattijo Dr. Shettima Ali Munguno bayan gama sallar jumu’a. Al’amarin ya kara dagula hankalin jama’a bayanda kungiyar Ahalis-Sunnah Lidda’awati wal Jihad ko Boko Haram, ta bada sanarwar cewa ba itace ta sace tsohon ministan man fetur din na farko na Nigeria ba. Wakilinmu a Maiduguri, Haruna Dauda, ya jiyo ta bakin mutanen jihar Borno kan rayuwa da halin Dr. Shettima Ali Munguno, kuma ga arhoton da ya aiko mana: