Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Korar Sama Da Mutane Dubu 12 Daga Inda Suke Zaune A Kenya


Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta

Hukumomi a kasar Kenya sun fara korar dubban mutane da suka ce sun mamayen gandun dajin Maasi Mau, inda tafkoki dake baiwa kogi dama da ruwa a yakin Afrika ta Gabas suke farowa.

Su 'yan kama wuri zaunar daga unguwar Kalejinin, sun ce wasu attajirai masu sayar da filaye sun damfaresu da takardun filaye na jabu. A cewar wakilin Muryar Amurka a yankin Narok, John Ndiso, yace babu wanda hukumomi suka gurfanar da shi gaban doka a kan wannan zargin damfara, haka zalika babu wata diya da aka biya wadanda ake korar.

Samuel Towett mazaunin gandun dajin Maasi Mau ne tsawon shekaru 30. Yace da yan sanda suka je wurin a farkon watan Yuli, sun lalata masa shagonsa na sayar da flawa wanda shi da matansa biyu da 'ya'yansa 14 suka dogara a kai domin samun abin masarufi.

Yace 'yan sanda sun isa wurin ne a cikin mota suka fara tarwatsa mutane, yace idan suka ganka to fa, ka shiga matsala domin zaka sha duka.

Sai dai 'yan sanda sun musunta yin amfani da karfin tuwo yayin da suka fara korar mutane da yawansu ya kai dubu 12 daga gandun dajin Maasi Mau.

Wannan dai ba shine karon farko da ake korar mutane daga wurin ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG