WASHINGTON, DC —
A karkashin shugabancin Sarkin Musulmi Alhaji Mohammad Sa'ad Abubakar III da Amir Hajjin bara Shehun Borno Umar Garbai El-Kanemi an yi taron duba ayyukan hajjin bara da kuma yadda za'a shirya yin na bana.
Taron ya duba nasarorin da aka cimma da kara kimtsawa domin bin ka'idar kujeru 76000 da hukumomin Saudiya suka baiwa kasar. Shugaban hukumar alhazan Muhammad Musa Bello ya yi murna domin ya ce da'ar alhazai sai karuwa ta keyi. Yace watakila ma sabili da haka ne jami'an Saudiya suka fara zuwa Najeriya suna tambayar yadda hukumar alhazan Najeriya ke tsara ayyukanta.
Abun farin ciki ne cewa ba'a samu matsala da alhazan Najeriya a ayyukan hajjin bara. Da akan samu alhazai suna zanga-zanga ko kuma suna daukan kaya fiye da abun da doka ta tanada kana a dinga tukawa dasu a filin shiga jirgin sama. Duk wadannan babu su yanzu. Wannan alama ce hukumomin alhazai a jihohi suna aikinsu yadda ya kamata. Babu shakka sun tarbiyantar da alhazan.
A lokacin taron malamai sun kara bayani kan darajar hajji. Shugaban Izala Sheikh Bala Lau yace haduwarsu zata fi kyau idan suka rungumi Kur'ani Mai Girma da Hadishin Manzon Allah (S.A.W.) Abun da zai hada kawunan malamai ke nan. Yace abun da Sarkin Musulmi ya keyi na ganin an hadu karkashin inuwa guda daga lokaci zuwa lokaci abun a yaba masa ne. Yace jakadan Saudiya ya shaida cewa aikin da malamai ke yi ya kawo canjin halayar alhazai daga Najeriya. Halayen alhazi ya canza domin malamai sun shiga cikinsu suna koya masu suna wayar da kawunansu kan ka'idojin ayyukan hajji. Aikin hajji ba zai ci nasara ba sai an hada kai da malamai an koyawa mutane abun da ya kaisu kasar Saudiya. Tunda tafiya ce ta addini to jagororin addini su ne ke da hakin haskawa alhazai yadda Mazon Allah ya yi aikin hajji.
Tijani Bala Kalarawi ya yi anfani da taron wurin gudanarda wani littafin nasiha da ya wallafa mai taken jagorancin al'umma ina aka nufa wuta ko aljanna. Kalarawi yace ya rubutawa Farfasa Jega yana son ya rabawa 'yan siyasa littafin kyauta domin su san nauyin shugabanci dake kansu.
Ga karin bayani.