Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sune Ƙashin Bayan Demokraɗiyya


Matasa sun taru suna wakoki
Matasa sun taru suna wakoki

An bayyana matasa a matsayin ƙashin bayan demokraɗiyya tsohon mai baiwa Gwamna shawara akan harkokin matasa Zubairu Badamasi Yunusa, ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da suka yi da wakilin muryar Amurka, Saleh Ashaka.

Yace ya furta haka ne domin duk abinda ake yin a shugabanci a kowace alkarya ko kuma ko wace ƙasa ana ƙoƙarin abinda za’a yi ne dan a inganta rayuwar matasa masu tasowa domin matasa sune manyan gobe saboda haka ya zama wajibi duk ko wace irin Gwamnati ta wanzu ko shugabanci da a ke so a kwatanta gaskiya da adalci, dole ne a waiwayi matasa kuma a kyautata mu su domin a inganta rayuwar su domin su zama sun koyi darasi daga shuwagabanin da suke kai dan suma shuwagabanin gobe.

Mai bada shawarar ya ci gaba da cewar sa duk mutunin da yake ɗan ƙasa nagari mai kishin ƙasa da al’ummar sa to zai zama ya sa ƙasar sa a zuciyar kuma ta zama itace a gaba fiye da abun da zai samu domin idan kace abin duniya zaka nema ai babu maganar kishin al’umar ka bare kishin ƙasar ka.

Ya ƙara da cewa ya kamata a ce mutun na son al’umarsa da ƙasar sa shima wannan wani farali ne daga cikin farillan rayuwar sa ko da Musulmi ne ko Kirista.

XS
SM
MD
LG