Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Kumallo Ke Sa Ni Latti - Inji Malamin Makaranta


Wani malamin makaranta da ma'aikatar kula da harkokin ilimi ta kama da laifin zuwa aiki latti har sau dari da goma sha daya a cikin shekaru biyu amma ta yafe masa ya fito fili ya bayyana dalilin da ya ke sa shi zuwa aiki latti.

A ranar sha tara ga watan agusta ne babban jami'in ma'aikatar kula da harkokin ilimi na yankin New Jersey ya yi watsi da takardar sallamar malamin daga aiki wadda hukumar makarantar da ya ke aiki ta gabatar dangane da zuwan sa aiki latti a yawancin lokuta.

Kamar yadda jami'in ya bayyana, ya yi kokarin jin tabakin malamin kafin ya rattaba hannu akan takardar, inda gogan naka ya kada baki ya ce "gaskiya ba laifi na bane, abincin da nake karyawa da shi kullum da safe ne ya sa haka."

Malamin mai suna Mr Anderson ya kara da cewar "kullum idan na fara cin abinci mantawa na ke da lokaci na gudu, shi yasa nake latti zuwa wurin aiki, amma kuma duk a cikin makarantar nan babu wanda ya fi ni iya aiki, kuma bana lattin shiga aji. Amma tunda haka ne zan daina yin karin kumallo daga gida".

Hukumar kula da harkokin ilimin ta yafe masa laifin amma ta ba shi horon dakatar wa daga aiki na wasu 'yan watanni, ta kuma jawo hankalin shugaban makarantar da cewa ya kamata tun daga farko ya kamata ta ba malamin takardar jan kunne da tunasarwa akan zuwan sa aiki latti. yanzu haka dai hukumar ta amince da kare kansa da yayi a yayin da ya dora laifin akan abinci.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG