A ranar Laraba 15 ga watan Yuli Fadar Shugaban Amurka ta White House ta nesanta kanta da sabuwar caccakar da aka yi wa Dr. Anthony Fauci, kwararre a fannin cututtuka masu yaduwa na Amurka, game da yadda ya tunkari annobar coronavirus, har ma wata makala da aka wallafa a jarida ta bayyana shigen wasu ra’ayoyin shugaba Donald Trump.
A makalar da aka wallafa a jaridar USA Today, Mai ba da shawara kan harkokin cinikayya a Fadar White House, Peter Navarro, ya ce Fauci "na da kyakkyawar dabi’a a idon jama’a, amma duk abubuwan da na tattauna da shi akai ba daidai ba ne a cewarsa.
Ko da ya ke, bayan da aka wallafa makalar, daraktar harkokin sadarwa a Fadar White House, Alyssa Farah, ta ce bayanin Navarro "bai bi ka’idojin White House da suka dace ba kuma wannan ra'ayin na Peter ne.
Facebook Forum