Masu shigar da karar sun ce sun sami korafi a kan hambararren shugaban kasar Mohamed Morsi da wadansu kusoshin kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi da suka hada da shugabanta, Mohammed Badie.
An yiwa Mr. Morsi daurin talala a wani wurin da ba a bayyana ba tunda aka sauke shi daga karagar mulki ranar 3 ga watan Yuli, sai dai har yanzu ba a tukume shi da wani laifi ba.
Masu shigar da karar basu bayyana wadanda suka shigar da korafin ba, da ya hada da leken asiri da kuma raunata tattalin arzikin kasar.
A halin da ake ciki kuma, magoya bayan hambararren shugaban kasar sun ci gaba da zaman dirshe a dandalin Rabaa el-Adawi jiya asabar, suka kuma lashi takobin ci gaba da zanga zanga har sai an maida Mr. Morsi daga karagar mulki.
Masu zanga zangar sun yi tururuwa a dandalin duk da kazamin zafi da ake fama da kuma azumi da suke ciki.