Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zabi Ramaphosa a Matsayin Sabon Shugaban Afirka Ta Kudu


Sabon shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa a lokaci da ya isa zauren majalisar dokokin kasar
Sabon shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa a lokaci da ya isa zauren majalisar dokokin kasar

An zabi mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban kasa da zai maye gurbin shugaba Jacob Zuma da ya yi murabus.

A yau Alhamis, ‘yan Majalisar dokokin Afirka ta Kudu sun zabi Cyril Ramaphosa, a matsayin sabon shugaban kasar a hukumance.

An zabi Ramaphosa ne ba tare da an kada kuri’a ba, lura da cewa shi kadai ne dan takara da aka zaba a majsaliar dokokin da ke Birnin Cape Town, a cewar babban mai shari’a Mogoeng Mogoeng, yayin da yake bayani ga 'yan majalisar.

Bayan wannan sanarwa ce, ‘yan majalisar suke barke da rera waka da rawa a wani yanayi na nuna farin cikinsu.

Zabin da aka yi wa Ramaphosa, na zuwa ne sa’oi kadan bayan da shugaba Jacob Zuma ya yi murabusa daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba.

Murabus din Zuma, na zuwa ne kwanaki kadan bayan da shugabannin jam’iyya mai mulki ta ANC, ta yanke shawarar cewa za ta janye shi daga mukaminsa a farkon makon nan.

Sun dauki wannan matsaya ce saboda acewarsu, sun gaji da korafe-korafen zargin cin hanci da rashawa da ake yi akan Zuma, cikin shekaru tara da ya yi yana mulkar kasar.

Jam’iyyar ta ANC har ila yau, ta nuna bacin ranta, kan yadda ake fuskantar komadar tattalin arziki a Afirka ta Kudu.

Yanzu haka, Ramaphosa zai fuskanci kalubale da dama, ciki har da batun farfado da tattalin arzikin kasar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG