Masu raji na kira ga Majalisa taki amincewa da mutanen da Kenyatta ya nada, ya kuma ‘kara yawan mata da matasa. Ga fassarar rahotan Real Ombour daga birnin Nairobi.
Masu zanga-zanga ‘dauke da kwalaye masu rubutun “Ka janye jerin sunayen da aka gabatar” yayin da suke maci zuwa Majalisa a birnin Nairobi na kasar Kenya.
Suna neman shugaban kasar shugaba Uhuru Kenyatta yayi gyara ga jerin sunayen ministocinsa da zai nada.
Mata shida ne kadai daga cikin mutane 21 da aka zaba a jerin ministocin. Kuma babu matasa, ‘yan tsakanin ‘yan shekaru 18 zuwa 35. Masu raji sunce mutum guda kadai aka zaba mai dauke da nakasa.
Sabeti Mboga, ‘ya ‘yan ta uku kuma tana da nakasa, itama ta shiga zanga-zangar, tana mai cewa.
Tace na fito ne domin yin zanga-zangar saboda gwamnati bata tunawa da su. Kuma muna so mu shiga harkokin gwamnati kamar kowa.”
Masu zanga-zangar dai sunce shguaba Kenyatta na neman ya sakawa ‘yan jam’iyyarsa mai mulki.
Mercy Jelimo jamia ce kula da harkokin shugabanci da mulki ne a cibiyar wayar da kan al’umma kan ilimi.
Facebook Forum