A Jamhuriyar Nijar jam’iyyun hamayya sun yi kira ga Shugaba Issuhu Mahamadu ya yi murabus, saboda zargin sa da gazawa wajen tafiyar da al’amuran mulki, musamman fannin tsaro, inda ‘yan ta’adda ke ci gaba da hallaka sojojin kasar. Sai dai magoya bayan shugaban na ganin wannan a matsayin wani kame-kame irin na wanda ya rasa madafa.
A wata sanarwar da suka fitar a yau dinnan Asabar, ‘yan Adawar, a karkashin inuwar kawancen FRDDR, sun bayyana damuwa a game da tabarbarewar tsaron da ake ciki a yanzu a kasar. Sun dora alhakin hakan a wuyar Shugaban kasar Issuhu Mahammadu, a cewar mai Magana da yawun jam’iyyar kawance FRDDR, Doudou Mahammadu.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin kasar, kuma Sakataren yada labaran jam’iyyar PNDS Tarayya, Iro Sani, da yake mayar da martani akan zargin, ya bayyana cewa rashin hujja ne ya sa ‘yan adawa irin wannan tunani.
Ya kara da cewa, babu kanshin gaskiya - hasali ma take-taken na ‘yan adawa na nuna cewa ba su shirya shiga zabubbuka masu zuwa ba.
Jam’iyun na FRDDR sun alakanta yanayin da ake ciki a yanzu da batun zabubbukan da ake saran gudanarwa a karshen shekarar 2020.
Wani binciken da majalisar dokokin kasar ta gudanar a kwanakin baya dangane da yadda aka kasafta kudaden sha’anin tsaro a Ma’aikatar Tsaro Ta Kasa da Ma’aikatar Cikin Gida, ya gano cewa an tafka barna sosai saboda haka jam’iyyun FRDDR suka bukaci ‘yan adawa a majalisar dokokin kasa su dauki matakan gabatar da rahoton wannan bincike a gaban kotu don ganin an hukunta masu hannu a wannan al’amari.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum