Miliyoyin yara ne suke fita aiki a maimakon makaranta ala tilas kowacce rana a Sudan domin talauci, a daya bagaren kuma saboda babu wadatattun azuzuwan da zai dauki duk yaran.
Matashi dan shekaru goma sha biyar da haihuwa Murtadha Al-Haj ya daina zuwa makaranta shekaru uku da suka gabata domin ya taimaki iyayensa neman na kalaci. Murtadha yana zaune da iyayensa a Khartoum baban birnin kasar, kuma a wuni daya yana samun kasa da kwatankwacin dalar Amurka $4. Wannan hali da yake ciki yana kokarin hana shi cimma burinsa na zama likita.
Ya ce a ko yaushe, mahaifiyata ta kan ce min, nan gaba idan al’amura sun inganta a rayuwar mu, zaka koma ka yi karatu har ka zama likita, amma kwatsam! Sai al’amuran siyasa suka kwabe wanda ya kai ga hambare gwamnati a Sudan.
Duk da yake al’amuran siyasa sun daidaita a Sudan, har yanzu tattalin arzikin kasar yana da rauni.
Facebook Forum