Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu A Wasu Hare Hare A Maiduguri


Da yammacin jiya da misalin karfe shida na maraice ne mazauna birnin Maiduguri suka fara jin karar wasu ababe masu fashewa kamar bam.

Mazauna birnin na Maiduguri sun kuma ji karar manya manyan bindigogi wanda daga bisani aka ce wasu manya manyan makamai ne da ake kira Rocket Launcher suka dinga fadawa kan jama'a, abinda yayi sanadin mutuwar mutane da dama da kuma raunata wasu.

A duk abinda ake ciki dai hukumomi ba su ce komai akai ba kuma manyan makaman sun cikigaba ta fadawa kan jama’a a anguwanni. Amma dai an ga jami’an sojoji da dama suna ta kai komo da kuma motoci masu daukar marasa lafiya suna ta zirga zirga a cikin Maiduguri.

Duk da cewa dai ba wanda ya san ta inda makaman suke fitowa, amma bayanai na nuna cewa makaman sun fada akan jama’a da dama. Misali, wani dattijo wanda ya fada kansa da jikokinsa guda biyar, inda biyu suka mutu nan take, sauran uku kuma suka raunata, su na karbar magani a asibiti.

A halin da ake ciki ana jiran hukumomi su yi karin bayani. Sannan a wani karin rahoto, sojojin Najeriya sun sake kwace garin Marte da kwanakin bayan nan kungiyar ‘yan Boko Haram ta kwace.

A saurari rahoto cikin sauti Haruna Dauda Biu:

Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu A Wasu Hare Hare A Maiduguri
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00


XS
SM
MD
LG