Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Bukukuwan Zagayowar Ranar 'Yancin Nijeriya A Jihar Oyo


Bukukuwan Ranar Samun 'Yancin Najeriya.
Bukukuwan Ranar Samun 'Yancin Najeriya.

Sabanin yadda ta kasance a wasu jihohin Nijeriya, a jihar Oyo ta Kudu maso gabashin Nijeriya an yi bukukuwan ranar 'yancin Nijeriya.

Gwamnan jihar Oyo Senator Abiola Ajimobi ya yi kira ga ‘yan siyasan Nijeriya da su yi koyi da ‘yan siyasar farko irin su Chief Obafemi Awolowo, Sir Abubakar Tafawa Balewa, Sir Ahmadu Bello, Herbart Marcauley da sauransu saboda siyasar kishin kasa su ka yi ba irin na yanzu mai cike da gaba da rashin fifita kasa bisa bukatun kai ba. Gwamnan ya fadi hakan ne a jawabinsa jiya Talata a wurin bikin zagayowar ranar samin yancin kan Nijeriya karo na 53 da aka yi a Dandalin Lekan Salami da ke birnin Badun. Gwamnan ya ce muddun ‘yan Nijeriya na sha’awar cigaba, sai sun koma kan tarihinsu.

Shi kuwa wanda ya zana tutar Nijeriya tun asali mai launin kore da fari da kore, dattijo Tayo Akinkumi y ace ya yi amfani ne da irin fahimtar da ya yi wa Nijeriya wajen gano basirar zana tutar da za ta dace da kasar.
Kungiyoyi da dama da su ka yi fareti a wurin bikin ranar ta samin ‘yancin kai sun hada da nau’ukan jami’an tsaro da ‘yan bautar kasa da dalibai da kuma kungiyoyin ‘yan kasuwa da dai sauransu.

Wakilinmu na jihar Oyo Hassan Ummaru Tambuwal ya ce sauran manyan da su ka halarci bikin har da Kwamishinan ‘Yansandan jihar Alhaji Abdulkadir Indabawa da kwamandan rundunan sojojin Nijeriya da ke Badun Janar Jibrin da sauransu. An yi bikin ne cikin tsauraran matakan tsaro.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG