Yan sanda a Arewacin Najeriya sunce mayakan Boko Haram sun bude wuta a wajen zaman makoki a jihar Adamawa, inda suka kashe akalla mutane 18.
Haka kuma jami’ai sunce wasu dayawa sun raunata a dalilin harin da aka akai a Kauyen Kuda dake wajen Madagali, haka kuma yawan mutanen da suka rasa rayukansu na iya karuwa.
Shaidu sunce ‘yan Boko Haram sun shiga kauyen ne kan babura suka kuma bude wuta kan masu zaman makokin. Sun kuma ce yawancin wadanda aka kashen mata ne da kananan yara.
Boko Haram ta kashe sama da mutane dubu 20 tun farkon kafuwar kungiyar a Arewacin Najeriya cikin shekara ta 2009. Kungiyar mai tsatstsauran ra’ayi dai tace tana son kafa daular islama.
A shekarar da ta gabata sojojin Najeriya sun kwato duk garuruwan da kungiyar Boko Haram ta kame cikin shekarun baya da taimakon kasashen dake makwabta da Najeriyar, amma kungiyar ta ci gaba da kai hare hare a Kasuwanni da sauran guraren da jama’a ke taruwa, wasu lokutan ma suna amfani ne da ‘yan mata wajen kunar bakin wake.