Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yabawa Shirin Sojojin Najeriya Na Yankunan Zamfara


Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Ranar Soja A Zamfara
Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Ranar Soja A Zamfara

Shugaba Mohammadu Buhari ya yaba tare da jinjinawa irin tsarin da sojojin Najeriya suka fito da shi domin yaki da ta’addancin dake addabar yankin Dan Sadau da sauran yankuna a jihar Zamfara, da kuma arewa maso yammacin kasar.

Barayin dabbobi da masu satar mutane da 'yan fashi sunyi shekaru suna addabar al’ummar wannan yankunana tare da tauye musu zaman lafiya.

Duk da yake an jinjina tare da yaba irin tsare tsaren da za ayi amfani da shi wajen samun nasarar wannan yaki da ta’addanci a yankin Zamfara da makwabtan jihohi. Sai dai wasu mutane na nuna damuwarsu kan cewa ba a hada da sarakunan gargajiya ba da ‘yan kungiyoyin banga da na tauri cikin tsare tsaren don samun nasarar yakin.

A cewar sanata Sa’idu Mohammed Dan Sadau, mutanen Zamfara musammanma na yankin Dan Sadau sun gani a kasa, domin irin kayan aikin da aka girke don tabbatar da an samar da zaman lafiya.

Saurari cikakken rahotan Umar Faruk Musa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG