Sojojin da ke mulki a Mali sun tsige Fira minista Dr Choguel Maiga daga mukaminsa tare da rusa gwamnatin da yake jagoranta bayan da ya zarge su da yin gaban kansu wajen gudanar da lamuran mulki.
Tuni aka maye gurbinsa da tsohon ministan ci gaban karkara Kanal Abdoulaye Maiga.
A jiya Laraba Dr. Choguel Maiga ya cewa shugaban mulkin sojin kasar, Janar Assimi Goita da mukarrabansa ba sa shawara da shi wajen daukan muhimman matakan gudanar da lamuran mulki.
Tsohon firai ministan ya bada misalin yadda suka dage babban zaben kasar da ya kamata a gudanar a shekarar nan ta 2024 ba tare da tuntubar mambobin gwamnati ba.
A yayin gangamin kungiyoyi da jam’iyyu mambobin kawancen M5 RFP da ya jagoranta a karshen mako a Bamako ne firai ministan ya fallasa yanayin rashin shawarar da ake fama da shi a tafiyar gwamnatin rikon kwaryar kasar.
Dandalin Mu Tattauna