Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sojojin Chadi 15 A Wata Arangama Da Mayakan Boko Haram


Chad soldiers vote early in the presidential election in N'djamena
Chad soldiers vote early in the presidential election in N'djamena

Akalla sojojin Chadi 15 ne suka rasa rayukansu, yayin da 32 suka ji rauni a wata arangama tsakanin sojojin kasar da ‘yan Boko Haram a ranar Asabar, kamar yadda mai magana da yawun sojojin ya bayyana, ya kara da cewa an kashe ‘yan Boko Haram 96.

A ranar Lahadi, Janar Issakh Acheikh, bai bayyana inda lamarin ya faru ba, hakazalika bai yi karin bayani game da yanayin arangamar.
Ya bayyana a gidan talabijin na kasar cewa sojojin sun kuma raunata ‘yan Boko Haram 11 tare da kwace makamai da kayan aiki.
“Rundunar sojanmu na tabbatar wa al’ummar kasar cewa an shawo kan lamarin, kuma ana ci gaba da daukar matakan farautar sauran mayakan, a zaman wani bangare na Operation Haskanite,” in ji Acheikh, yayin da yake magana kan aikin da sojojin suka kaddamar domin fatattakar mayakan Boko Haram daga tafkin Chadi.
Yankin dai ya sha fuskantar hare-haren ta’addanci da suka hada da na kungiyar IS a yankin yammacin Afirka da kuma Boko Haram, kungiyar da ta bullo a arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2009 ta kuma bazu zuwa yammacin kasar Chadi.
Kimanin sojoji 40 ne aka kashe a wani hari da aka kai a wani sansanin soji da ke yankin tafkin Chadi a karshen watan da ya gabata, bayan harin shugaban rikon kwarya na kasar Mahamat Idriss Deby, ya yi barazanar janye kasar daga cikin rundunar dakarun kasa da kasa ta yankin.
Kasar Chadi muhimmiyar kasar kawancen dakarun Faransa da Amurka ce, kasashen da ke neman taimaka wa wajen yakar mayakan sa-kai a yankin kudu da hamadar Sahara tsawon shekaru 12.
Gwamnatocin soja da suka kwace mulki a shekarun baya-bayan nan a Mali, Burkina Faso da Nijar, wadanda iyakokinsu suka zama wurin da tashin hankalin masu jihadi ya fi muni, sun juya wa kasashen yammacin duniya baya, maimakon haka suka rungumi Rasha.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG