NIGER, NIGERIA - Kabilar ta Kamabari dai wadanda aka bayyana cewa yawansu ya kai 172,000, akasarinsu suna sana’ar Noma da Kiwo ne a jihohin Naija, Nasarawa da Kebbi.
Shugaban kungiyar kabilar ta Kambarin a Najeriya Farfesa Muhammad Yakubu Auna, ya ce suna maida hankali ne wajan wayar da kan kabilar kan muhimmancin zaman lafiya da kaunar juna da kuma kaucewa aikata miyagun ayuka da zai shafi kasa.
Shugaban kungiyar kiristoci ta CAN a jihar Neja Bishop Bulus Yohanna, wanda shi ma dan kabilar Kambarin ne da yahalarci taron da aka gudanar a garin Kontagora, ya ce sai da zaman lafiya ne kowacce kabila za ta sami ci gaba.
Sai dai akwai matsaloli da suka ce ana fama da su musamman ga ‘yan uwansu mazauna yankunan karkara. Shugabar mata ta kugiyar ta ce hatta kananan asibitoci a karkara sun yi karanci ta yadda hakan ke janyo asarar rayukan mata.
‘Dan majalisar wakilan Najeriya Shehu Sale Rijau ya ce suna kara fadakarwa kan muhimmancin neman ilmi da illar shan miyagun kwayoyi.
Gwamnatin jihar Nejan dai ta ce tana farin ciki da ‘yan kabilar Kambarin akan yadda suka rungumi zaman lafiya. Hon. Baba Suleiman Yumu, kwamishinan harkokin bada agaji na jihar ne ya wakilci Gwamnan jihar a wannan taron.
Daga bisani an raba kyaututtuka ga makadan gargajiya na kabilar da suka zama zakaru a gasar da aka fafata a wajen taron.
Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:
Dandalin Mu Tattauna