Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sauya Firai Minastan Kasar Haiti Da Ke Fama Da Rikicin Siyasa


Ceremony to install Transition Council
Ceremony to install Transition Council

Majalisar rikon kwarya da aka kafa don sake maido da tsarin dimokuradiyya a Haiti, ta sanya hannu kan wata sanarwa, inda ta kori Firai Ministan kasar na rikon kwarya, Garry Conille tare da maye gurbinsa da Alix Didier Fils-Aimé, wani dan kasuwa wanda a baya aka yi tunanin ba shi mukamin.

Wata majiyar gwamnati ce ta ba kamfanin dillancin labaran Associated Press sanarwar, da za a wallafa ranar Litinin. Hakan ya kara nuna irin rikicin da ke tattare da shirin komawa ga mulkin dimokiradiyya a Haiti, inda ba a gudanar da zabukan dimokuradiyya ba cikin shekaru da yawa, galibi saboda yawan tashin hankalin kungiyoyin miyagu da ke addabar kasar da ke yankin Karebiya.

Fils-Aimé, shi ne tsohon shugaban hukumar harkokin kasuwanci da masana'antu ta Haiti kuma a shekarar 2015 ya nemi takarar kujerar dan majalisar dattawa amma bai yi nasara ba. Dan kasuwan ya yi karatu a Jami'ar Boston kuma a baya an yi tunanin ba shi mukamin kafin a ba Conille.

Conille, wanda ya dade a matsayin ma'aikacin gwamnati wanda ya yi aiki da Majalisar Dinkin Duniya, ya yi aiki a matsayin Firai minista ne tsawon watanni shida kacal.

A watan Afrilu ne aka kafa majalisar rikon kwaryar, wadda aka dorawa alhakin zabar Firai ministan Haiti da majalisar ministocinsa da nufin taimakawa wajen kwantar da tarzomar da kasar ke fuskanta. Amma majalisar ta fuskanci rigingimun siyasa da takaddama kuma tuni ta fara sa'in-sa da Conille.

A makon da ya gabata kungiyoyi kamar Organization of American States, sun yi kokarin shiga tsakani a wani yunkuri na ceto shirin komawa dimokradiyyar mai rauni, a cewar wani rahoton jaridar The Miami Herald.
Shirin komawa dimokradiyyar ya sake fuskantar koma baya a watan Oktoba, a lokacin da mambobin majalisar 3 suka fuskanci zarge-zargen cin hanci da rashawa daga masu bincike kan yaki da cin hanci da rashawa, inda suka yi zargin cewa sun nemi cin hancin dala 750,000 daga wani daraktan bankin gwamnati don kare mishi aikinsa.

Wadannan mutanen 3 da aka zarga da cin hanci, Smith Augustin, Emmanuel Vertilaire da Louis Gérald Gilles, na daga cikin wadanda suka sanya hannu a sanarwar umurnin. Mutum daya a majalisar Edgard Leblanc Fils ne bai sanya hannu a takardar ba.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG