Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Raguwar Rashin Aikin Yi A Najeriya


Hukumar ƙididdiga da tattara bayanai akan tattalin arzikin Najeriya ( National Bureau of Statistics)
Hukumar ƙididdiga da tattara bayanai akan tattalin arzikin Najeriya ( National Bureau of Statistics)

Hukumar kididdiga da tattara bayanai akan tattalin arzikin Najeriya ta fitar da sanarwa da ta ya bayyana cewa, rashin aikin yi ya ragu a tsakanin 'ƴan Najeriya.

Wannan alkalumar da hukumar ta fitar ya biyo bayan irin tsadar rayuwa da 'yan Najeriya ke fama dashi tun bayan rantsar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Tun bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu yayi a ranar rantsuwar kama aiki, al'ummar kasar suka shiga matsin tattalin arziki, inda kayan masarufi ke hauhawa babu kakkautawa, sufurin mota yayi tsadar da bai taba yi a kasar ba.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Hatta ɗan abinda mutane ke kaiwa bakin salati ya fara gagara bisa karancin kayan cimaka, wanda hakan na nuna cewa, rayuwa tayi tsanani, duk da cewa Gwamnatin ta Shugaba Tinubu ta fito da tsare-tsare na ragewa al'ummar Ƙasar raɗaɗin da suke fama dashi.

A wata sanarwa da hukumar ƙididdiga ta Ƙasa wato (Nigeria Bureau Of Statistics) ta fitar, Hukumar ta ce an samu raguwar rashin aikin yi da kaso 4.1 idan aka kwatanta da kaso 5.3 na karshen shekarar 2022.

Semiyo Adediran, wanda shine babban Daraktan Hukumar, ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a lokacin kaddamar da rahoton a ranar Alhamis a birnin Abuja.

Daraktan, ya ce sun yi amfani ne da sabon alkaluman kididdigar a Najeriya, wanda yanzu ya zama iri ɗaya da ta sauran ƙasashen duniya.

Ya ƙara da cewa wannan ƙididdigar anyi ta ne da hadin gwiwar Bankin Duniya da ƙungiyar ƙwadago ta Duniya (ILO).

A hirar shi da Muryar Amurka, Dakta Ahmad Abdullahi Bukata Malami a tsangayar ilimin tattalin arziki a Jami'ar Bayero dake jihar Kano, ya bayyana cewa labarin wannan ƙididdiga a takarda abu ne mai dadin ji, kuma cigaba ne da za'ayi fatan ɗorewarsa, sai dai a zahiri mutane suna ji a jikinsu, kuma sahihanci ƙididdiga a ƙasashe masu tasowa ba abin farin ciki bane, saboda rashin ingancin sa.

A gefe guda kuma, 'yan Najeriya sun bayyana cewa, wannan ƙididdiga a takarda suka san shi, domin har yanzu rashin aikin yi a Najeriya bata canza zani ba.

Idan za'a iya tunawa a baya hukumar ta ce za ta yi amfani da sabuwar hanyar kididdiga wajen sanin ainihin yawan masu aikin yi da masu zaman ɗumama benci, domin samun sahihancin alkaluma a Ƙasar.

Irin wannan ƙididdiga da alƙaluma na bayanai masu faranta rai ba sabon abu bane a ƙasashe masu tasowa, sai dai a zahirance jirwaye ne me kamar wanka.

Saurari rahoton Ruƙaiya Basha:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG