Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Karuwar Yawan 'Yan Gudun Hijira a Duniya


A jiya Alhamis ne, Shugaban Hukumar Kula da 'yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi ya ce an samu karuwar 'yan gudun hijra sama da miliyan saba’in a fadin duniya baki daya, inda ya kira wannan da “wata babbar gazawa" ga al'ummar duniya, sannan ya yi kiran da a hada kai a duniya baki daya wajen warware wannan matsalar.

“Yawancin mutane miliyan 70 din da muke Magana kansu sun guje wa yaki da tashe-tashen hakula ne daga kasashen su."

Grandi ya fadawa wa Muryar Amurka a wata tattaunawa da ta yi da shi a Amman na kasar Jordan, yayin da ake bikin ranar yan gudun hijira ta duniya, cewa da alamar dai al'ummar duniya ta daina la’akari da yadda za’a shawo kan wannan matsalar.

Hukumar yan gudun hijira ta MDD ta fada a cikin wannan satin cewa mutane miliyan saba’in da dubu dari takwas, ne a bara sukai kaura daga muhallansu saboda tsananin yaki, da rashin yanci da kuma mawuyacin hali, inda ya haura mutane 2.3 a shekarar 2017.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG