Wata tawagar kwararru da ke karkashin jagorancin kasar Netherland wacce ke bincike kan jirgin fasinjar Malaysia da aka harbo a sararin samaniyar kasar Ukraine a shekarar 2014, ta bayyana sunayen wasu ‘yan kasar Rasha uku da wani dan kasar Ukraine daya, a matsayin wadanda ake zargi da aikata kisa.
Babban mai shigar da kara na kasar ta Netherland, Fred Westerbeke, ya fada a wani taron manema labarai a birnin Hague a yau cewa, wadanda ake zargin, sun taka rawa wajen harbo jirgin mai lamba MH17, duk da cewa ba sune suka danna maballin da ya kakkabo jirgin ba.
Amma ana zargin cewa sun taka munimmiyar rawa wajen samo makami mai linzamin da aka yi amfani da shi wajen harbo jirgin.
Mutanen da ake zargin sun hada da Igor Girkin, Sergey Dubinskiy da Oleg Pulatov wadanda duk ‘yan Rasha ne, sai kuma dan kasar Ukraine Leonid Karchenko.
Facebook Forum