Shugabar Hong Kong mai goyon bayan China, Carrie Lam, ta bayar da hakuri jiya Talata game da rikicin siyasa da tashin hankalin da ya faru sakamakon wani kudurin doka da zai bada damar a dauki mai laifi zuwa kasar China domin yi masa shari’a. Amma ba ta amsa kiran masu zanga-zanga ba, na neman ta sauka daga mukaminta kan yadda ta tafiyar da lamarin kudurin dokar da ya janyo cece-kuce.
Lam ta fada wa manema labarai cewa an dakatar da aiki kan kudurin har sai lokacinsa ya kare a watan Yulin shekara mai zuwa, amma ta kuma sha alwashin tsayawa da kammala sauran wa’adinta a kan mulki.
“Na ji ku ‘karara kuma na yi dana sanin abin da ya faru,” a cewar Lam, ta kuma ‘kara da cewa ita da kanta ta dauki alhakin abin da ya faru akan kudurin dokar.
Facebook Forum