Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Cuba Zai Hada Kai da Amurka Don Yaki da Ebola


Tsohon shugaban kasar Cuba, Fidel Castro.
Tsohon shugaban kasar Cuba, Fidel Castro.

Tsohon shugaban kasar Cuba, Fidel Castro ya ce cikin farin ciki kasar shi za ta hada kai da Amurka su yaki cutar Ebola a Yammacin Afirka.

Tsohon shugaban kasar Cuba, Fidel Castro ya ce cikin farin ciki kasar shi za ta hada kai da Amurka su yaki cutar Ebola a Yammacin Afirka.

Tsohon shugaban kasar na Cuba mai shekaru 88 ya ce hadin kai ne domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, ba wai wani kokari ne na neman warware matsalolin dake tsakanin Amurka da Cuba ba.

Fidel Castro ya ce cikin farin ciki za su hada kai da ma'aikatan Amurka a cikin wannan aiki, ya ce ba don neman zaman lafiya tsakanin kasashen biyu ba wadanda suka dade su na gaba da juna, ya ce amma duk abun da ya faru ko zai faru, saboda zaman lafiya ne da kwanciyar hankali a duniya, wanda ya ce wani buri wanda ake iya cimma wanda kuma ya kamata a yi kokarin cimma.

Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry ya yabawa kasar Cuba saboda gagarumin matakin da ta dauka na taimakawa kasashe masu fama da Ebola, ya ce kasar Cuba mai yawan jama'a miliyan 11 kawai, amma har ta tura kwararrun likitoci 165, kuma ta na shirin kara tura wasu kusan 300 zuwa kasashen Yammacin Afirka da suka fi jin jiki saboda cutar ta Ebola.

Tarihi ya nuna cewa Cuba ta saba tura likitocin ta su kai daukin gagawa a ko'ina a duniya.

Tun zamanin juyin juya halin shekarar 1959 wanda ya kai Fidel Castro ga mulki, Cuba ta ke tura rundunonin likitocin ta wuraren da bala'o'i ke fadawa a fadin duniya.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce cutar Ebola ta kashe mutane fiye da 4,500 a yammacin Afirka. Kuma kwararrun likitoci sun yi hasashen cewa kafin karshen shekara karin wasu dubban mutanen na iya mutuwa sanadiyar cutar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG