Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Raguwar Mutuwar Mata Da Kananan Yara A Najeriya


Wata mata da karamin yaro
Wata mata da karamin yaro

Hukumar lafiya ta duniya ta yabawa Najeriya domin ci gaba da ta samu wajen kula da lafiyar mata da kananan yara.

Hukumar lafiya ta duniya ta yabawa Najeriya domin ci gaba da ta samu wajen kula da lafiyar mata da kananan yara.

Hukumar ta yaba shirin da Najeriya ta kaddamar shekarar da ta wuce da nufin ceton rayuka mata da kananan yara miliyan daya bara da taken, “Save Million Lives Initiative” wanda shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kaddamar shekarar ta ta wuce.

A karkashin wannan shirin, Najeriya ta sami nasarar ceton rayukan mata masu ciki, miliyan daya kuma suka fara zuwa awo, yayinda kuma aka ba yara miliyan arba’in da shida wadanda shekarunsu basu kai biyar ba sinadarin bitamin A, aka kuma yiwa kashi 78% na kananan yara rigakafi.

A cikin jawabinsa wajen taron lafiya na duniya karo na sittin da shida, karamin ministan lafiya Mohammed Ali Fate yace gwamnati ta fara da maida hankali wajen gano dalilan mace macen mata da kananan yara ta kuma dauki matakan gaggawa wajen shawo kan matsalolin da suka hada da rashin unguwar zoma da kuma dakunan kula da mata.

Ministan ya bayyana cewa an dauki ma’aikatan jinya dubu shida aka kuma kaddamar wa dani shirin aikin jinya tare da ba mata tukuici da nufin karfafa masu guiwa su rika zuwa awo ko kuma kai ‘ya’yansu asibiti su.
XS
SM
MD
LG