Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kusa Samun Maganin Zazzabin Cizon Sauro Mai Karfi


Wata yarinya mai fama da zazzabin cizon sauro
Wata yarinya mai fama da zazzabin cizon sauro
Masu ilimin kimiyya sun samu cin gaba a neman maganin da zai iya kashe zazzabin cizon sauro da za a sha sau daya kawai ba kari, wanda banda jinyar wanda ya kamu da cutar, zai kuma zama rigakafi da garkuwa ga wanda ya sha maganin.

Ana kyautata zaton za a fara gwajin kaifin maganin ne a karshen wannan shekarar ta dubu biyu da goma sha uku wanda ake gani zai taimaka wajen ceton rayukan miliyoyin mutane a kasashen nahiyar Afrika.

Wannan ne maganin farko da za a sarrafa daga binciken da aka faro a Afrika da ‘yan nahiyar Afrika da kansu suka gudanar.

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana zazzabin cizon sauro a matsayin cutar da tafi kowacce kisa, da take kashe kimanin mutane miliyan daya da dubu dari biyu kowacce shekara da suka hada da kananan yara da shekarunsu basu kai biyar ba, da kuma mata masu ciki.

Najeriya tafi kowacce kasa a duniya fama da zazzabi cizon sauro inda kimanin mutane dubu dari uku suke mutuwa da dalilin kamuwa da cutar kowacce shekara.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG