Jirgin wanda ya taso daga kasar Mozambique da fasinja 27 da ma’aikatansa su 6 ya yi niyyar sauka ne a Luanda, babban birnin kasar Angola a jiya Jumma’a.
Bayan da aka ba da rahoton bacewar jirgin, sai aka shiga wani dogon bincike wanda ya kai ga gano baraguzan jirgin da ya kone a yau dinnan Asabar cikin kurmin da ke cikin gandun dajin kasa na Bwabwata, wanda ke kusa da kan iyakar Angola da Botswana.
Nan take dai ba a bayyana abin da ake ganin ya haddasa faduwar jirgin ba.
Hukumomi sun ce mamatan sun hada da ‘yan Mozambique 10 da ‘yan Angola tara da ‘yan Portugal biyar da wani dan Faransa da dan Brazil da kuma dan China. Ba a bayyana kasashen da sauran mutane shidda su ka fito ba, wadanda ga dukkan alamu ma’aikatan jirgin ne.
A halin da ake ciki kuma masu ayyukan ceto sun tabbatar da mutuwar mutane takwas, bayan da wani jirgin sama mai saukar ungula ya fa fada kan wata mashayar Scottland. Hukumomi na kyautata zaton za a sami karin mace-mace.
‘Yan sanda a Glasgow sun ce wani jirgin sama mai saukar ungula mallakin ‘yan sanda ne ya rikito kan mashayar da yammacin jiya Jumma’a a yayin wasu kide-kide da raye-raye wanda ya watsar da dinbin baraguzan da su ka mamaye wuri mai fadi.
‘Yan sandan da ke wurin sun ce su na fama ne da wani hadari mai girma. Shaidu suna ganin ma wasu ‘yan fatarol sun makale a wannan benen mai hawa daya.
Babu alamar wuta, kuma shaidu sun ce babu wata fashewa. An hango farfalan jirgin na rito a kan ginin bayan faduwar jirgin.
Hukumomi sun ce akwai wasu jami’an ‘yan sanda biyu da Kyaftin din jirgin, wanda farar hula ne a cikin jirgin.