Kwanaki uku a bayan da mahaukaciyar guguwar teku mai suna Typhoon Haiyan ta hauro kan doron kasa, har yanzu hukumomin Philippines su na kokari ne ma su gano irin barnar da ta haddasa.
A wani gefe, jiragen sufurin kaya na sojojin Amurka tare da wata bataliyar sojojin kundumbala sun isa kasar ta Philippines domin taimakawa.
Wakilin Muryar Amurka a yankin arewa maso gabashin Asiya, Daniel Schearf, yace jiragen sama masu saukar ungulu sun fara jigilar kayayyakin abincin gaggawa, da ruwan sha da wasu kayan na masarufi da bukatun yau da kullum zuwa yankin tsakiyar Philippines wanda mahaukaciyar guguwar ta yi ma kaca-kaca, kwanaki uku bayan da ta ratsa ta yankin.
Ga Ibrahim Alfa Ahmed dauke da fassarar rahoton na Daniel Schearf.