Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiya Ta Bude Sabon Silima Bayan Shekaru 35


Bayan shekaru 35 da aka haramta bude gidajen kallon fina finai, kasar Saudiya ta bude gidan kallo na silima kuma an fara budewa ne da nuna sabon fim din nan mai farin jini mai suna Black Panther a sirrance.

Gayyatar da aka bayar kawai ta bikin gala a taron da aka yi a dakin taro a Riyadh ranar laraba shine na farko a gwaje gwajen fina finai da aka fara yi, kuma an baiwa kamfanin fina finan Amurka AMC lasisin aiki a gidajen cinema. An daga takunkumin da aka sanya wanda ya sa aka rufe gidajen kallo a Saudiya a shekarar 2017.

Shugaban AMC Adam Aron, ya ce za’a fara sayar da tikiti jiya laraba inda kowa da kowa zai iya zuwa yayi kallo to amma jami’an cikin gida a Saudiya sun nuna cewa gwaje gwajen zai dau ‘yan kwanaki ana yi. Kwanan baya dai ma’aikata suka ce suna sa ran bude cinama ga al’umma baki daya a watan mayu.

Wannan rana ce da AMC zata tuna a tarihi, wannan ranar tarihi ce ga kasar ku,’’ a cewar Aron, lokacin da yake wa jami’an gwamnati da wasu ma’aikata bayani. Yace muna muku marhaba lale da shigowar lokaci da ‘yan saudiya za su yi kallo a gidajen kallo a kasar su ba sai sun je Bahrain ba, ba a Dubai ba ko ingila amma a cikin daular kasar su Saudiya.

Sake bude gidajen kallon Sinima a Saudiya wani mataki ne da yarima Mohammed bin Salman ya dauka, na kawo change chanje da ke tafiya da zamani, duba da yadda yake neman kawo daidaito saboda yadda kudin man fetur yayi kasa. Duk da rashin amincewar masu suka.

Saudiya dai ta dau hanyar chanje chanje da zamani ya zo dashi, kamar barin mata su fara tuki da barin mata da maza halartar taro a gudaya sabanin da.

Jaridar The Gaurdian ta Amurka ta ruwaito.

  • 16x9 Image

    Hafsat Muhammed

    Hafsat Muhammed, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG